Friday, 23 March 2018

'Zan sake rubuta wata wasika game da abubuwan dake gudana a Najeriya'>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa irin yanda abubuwa ke tafiya a kasarnan basu mai dadai dan haka yana tunanun kara rubuta wata wasika irin wadda ya rubuta a kwanakin baya yana caccakar gwamnatin shugaba Buhari akan salon mulkintan , Abinda ya dauki hankula sosai.


Obasanjo ya bayyana hakane a garin Legas gurin wani taro akan cigaban mata, kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaita, ya kara da cewa idan ya rubuta wannan wasikar zai jima be kara rubuta wata ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa, kungiyar da ya bude dan ceto Najeriya daga halin ha'ula'in da take ciki ta samu mutane miliyan uku da suka yi rigista haddashi dan haka ya nuna farin cikinshi da wannan cigaba da suka samu.

No comments:

Post a Comment