Friday, 20 April 2018

'A daren da mijinta ya mutu, Maryam Sanda tayi yunkurin caka mai wuka da fasassar kwalba sau 3'>>inji shaida

A cigaba da shari'ar matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, Alkalin kotun ya fara sauraron shaida na farko da ya bayyana abinda ya sani dangane da kisan mijin Maryam din watau Bilyaminu Bello da a gurin tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello.


Ibrahim Muhammad wanda abokine ga marigayin yace suna tare da Bilyaminu daren da aka kasheshi, yace suna zaune suna shan shisha a falon Bilyaminun suna kallo sai Maryam ta kirashi daga saman bene, Bilyaminu yaje ya sameta, bayan wani dan lokaci sai ya fito falo suka cigaba da hira, can kuma sai ga maryam din da kanta ta sakko kasa ta kira Bilyaminun, Ibrahim ya kara da cewa can sai yaji hayaniya ta kaure tsakanin Maryam din da Bilyaminu, Maryam ta aiko aka kirashi.

Yana zuwa sai ya same su sunci kwalar juna,  ya tambayesu meke faruwa haka, Maryam tace mai ya gayawa abokinshi ya saketa, ya rokesu suyi hakuri, Maryam tace babu inda zata sai ya saketa, nan dai yayi kokari ya rabasu, suka saki juna.

Can kawai sai Maryam ta dauki kwalba ta fasa ta nufi Bilayminu tace ya sake ta ko kuma ta yankemai mazakuta, nan suka samu suka kwace fasassar kwalbar daga hannunta, Shi kuma Bilyaminu ya fita daga dakin, Muhammad yace nan ya zauna ya fara baiwa Maryam hakuri akan suyi hakuri da juna suna haka sai ga Bilyaminu ya shigo dakin.
Maryam ta sake tashi ta nufeshi da wata kwalbar data fasa tana cewa ya saketa ko ta yankemai maza kutarshi, nan dai Bilya bece komai ba ya kwace kwalbar ya nufi falo.

Can kuma Maryam ta sake dauko wuka daga dakin dafa abinci ta nufi Bilya da ita itama ya kwace, ta sake daukar wata suka kama kici-kici, nan dai ya samu ya sake kwacewa, Muhammad yace kusan sau uku maryam na yunkurin illata Bilya.

Da ya ga abin yaki ci yaki cinyewa sai ya kira wani abokinsu bayan da ya zo sai suka fita shi da bilyaminu aka dubamai ciwukan da Maryam din ta ji mishi.

Da suka dawo gidan bata nan sai kuma gata ta dawo ta koma tana wasa da diyarta, nan dai suka tafi suka barsu haka, Muhammad na bada labarin abinda ya faru da ga dayan abokinshi kamin yazo.

Muhammad ya kara da cewa bayan da suka tafi sunyi kokarin sake kiran Bilyaminu amma basu sameshi ba, sai daga baya aka kirasu akace Bilyaminu ya mutu.

Muhammad ya kara da cewa nan ya tafi asibitin Maitama inda ya iske gawar abokinshi da dangin matar dana shi.

Muhammad ya kara da cewa a duk lokutan da Maryam ke dauko wuka bata furta cewa zata kashe Bilyaminuba, kawai dai tace zata yankemai mazakutane.

Bayan sauraron shedar Alkalin kotun ya daga shari'ar zuwa ranar 15 ga wayan Mayu.
Dailypost.

No comments:

Post a Comment