Sunday, 15 April 2018

A'isha Buhari ce gwarzuwar shekara ta jaridar Vanguard: Ta jaddada goyon bayanta ga mijinta Shugaba Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buharice ta amshi kyautar karramawa ta gwarzuwar shekara ta jaridar Vanguard, diyarta, Halima Sharif ce ta wakilceta a gurin taron da akayi jiya a otal din Eko dake birnin Legas.


A jawabin da tayi a gurin taron, A'isha ta bayyana cewa tayi matukar farin ciki da samun wannan kyautar karramawa da batayi tsammani ba wadda aka bata lura da irin taimakon da takewa marasa galihu musamman mata, yara da matasa ta bangaren kiwon lafiya da sana'o'i da ilimi.

A'isha Buhari ta jaddada goyon bayan ta ga mijinta Shugaba Buhari inda tace maganar da tayi akan salon mulkinshi wanda yana daya daga cikin abubuwan da aka lura dasu kamin bata wannan kyauta, ba tayi bane dan nuna rashin da'a ko kuma yin fito na fito da kowa ba amma dai tayi hakanne kawai dan fadar gaskiya, domin irin tarbiyyar da aka mata kenan.

No comments:

Post a Comment