Wednesday, 11 April 2018

A'isha Buhari tayi kira ga asibitoci masu zaman kansu da su rage kudin ayyukansu

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta amshi bakuncin kungiyar ma'aikatan asibitocin gwamnati dana masu zaman kansu da suka kaimata ziyara a fadar shugaban kasa yau Laraba, A'isha Buhari tayi kira ga asibitoci masu zaman kansu da su rage yawan kudin ayyukan da suke wa jama'a ta yanda za'a samu sauki.


Ta bayyana cewa da dama akwai wadanda ke zuwa asibitocin kudi saboda rashin isassun asibitocin gwamnati kuma wasu lokutan kudin aiki na da tsada dan haka tayi kira ga masu asibitocin kudin dasu rage yawan kudin ayyukansu, Hajiya A'isha ta kuma yi kira ga inganta yanayin ayyukan likitoci a kasarnan dan rage yawaitar komawar likitocin kasashen waje kuma 'yan Najeriya suna binsu can suna musu aiki.

No comments:

Post a Comment