Thursday, 5 April 2018

Allahu Akbar: Ana tsaka da kwallo: Daya lura lokacin Sallah yayi: Muhammad Salah yayi lambon karya dan a fitar dashi yaje yayi Sallah

A wasan da suka buga jiya na gasar cin kofin zakarun turai tsakanin Liverpool da Manchester City, dan wasan kungiyar Mohammad Salah ya fara zura kwallo a ragar Man City inda Chamberlain da Sadio Mane suma suka zura kwallaye, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci  kuma ya lura lokacin sallah yayi, Muhammad Salah yayi lambon karya dan a cireshi yaje yayi sallar Isha.


Ana cikin mintuna hamsin da biyu na dawowa daga hutun rabin kokaci Sai Muhammad Salah ya nuna alamar baya jin dadi, hakan yasa dole aka canjashi, to saidai wasu 'yan kallo  musulmai sun lura da cewa a daidai lokacin da Salah din ya nuna baya jin dadi lokacin Sallar Isha ne yayi dan haka da yawa suka yi ittifakin cewa lambon karyane Salah din yayi dan ya samu yayi Sallar.

Wasu alamu dake kara tabbatar da hakan sune bayan da aka kammala wasan an tambayi kocin Liverpool din, Klopp ko me zaice dangane da ciwon da Salah din ya nuna yana ji?


Sai ya kada baki yace Eh ya nuna mishi baya jin dadi yayin da ake tsaka da wasa dan haka dole ya canjashi, amma bayan da aka kammala wasan ya tambayi Salah din ya yake jin jikinshi, sai ya shaidamai cewa ya warware ba wata matsala.

Amma Klopp ya kara da cewa duk da haka ba zasu iya tabbatar da cikakkiyar lafiyar ta Salah ba sai likitoci sun dubashi sun basu rahoto a hukumance tukuna., kamar yanda Skysport da Independent da kasar Ingila suka ruwaito.

Wasan dai ya kare Liverpool na da 3 Mancity kuwa na da 0.

Salah dai be bayyana cewa Son yin sallah ne yasa shi yin lambo amma da yawa daga cikin 'yan kallo musulmai sunyi ittifakin hakan kuma sun yabeshi da kasancewa musulmi na gari.

Muna mishi fatan alheri

No comments:

Post a Comment