Saturday, 7 April 2018

An Bayarda Belin Salman Khan

Wata kotu a kasar India ta bayar da belin jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, wanda ta yanke wa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.
                             
 Ranar Alhamis Din Da Ta Gabata ne kotun ta yanke wa jarumin hukuncin bisa samunsa da laifin yin farautar gwankin da ba kasafai ake samunsa ba, ba bisa ka'ida ba.
Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.
Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Tun da fari dai, lauyan jarumin mai shekara 52, ya gabatar wa kotun hanzarin mutumin da yake  Wakilta A cewarsa, daurin shekara biyar zai haifar da koma-baya a sana'arsa ta fim.
Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

bbchausa

No comments:

Post a Comment