Saturday, 21 April 2018

An samu karin matan dake lakadawa mazajensu duka a jihar Legas

Kwamishinan shari'a na jihar Legas ya bayyanawa manema labarai cewa sun samu karin korafe-korafen mata dake lakadawa mazajensu duka a jihar idan aka kwatanta da kararrakin da aka kawo shekarar data gabata.


Adeniji Kazeem ya kara da cewa an samu karin korafe-korafe gudan talatin da takwas akan wanda ake dasu ada, kamar yanda jaridar Newtelegraph ta ruwaito

No comments:

Post a Comment