Wednesday, 4 April 2018

An Tashi Baran - Baran A Taron Gwamnonin APC Da Buhari

Rahotanni daga Fadar Shugaban kasa sun tabbatar da cewa an tashi baran baran a taron da Shugaba Buhari ya yi da gwamnonin APC a yau game da cimma matsaya kan batun tsawaita wa'adin shugabannin APC.


An dai fara taron ne da misalin karfe biyu na rana wanda makasudin taron shi ne yadda za a rusa shugabannin jam'iyyar a karkashin jagorancin Cif John Odigie-Oyegun tare da kafa kwamitin riko a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Edo, Adam Oshiomhole.

Sai dai kuma mafi rinjayen gwamnonin sun goyi bayan karawa shugabannin wa'ad a maimakon rusa su. Rahotannin sun nuna cewa, a karshe Shugaba Buhari ya fice daga zauren taron inda ya bar gwamnonin su sake saka ranar sake taron wanda kuma Shugaban Kungiyar Gwamnoni kuma Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya saka ranar 9 ga wannan wata sai dai kuma Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya kalubalance shi kan saka wannan ranar.
rariya.

No comments:

Post a Comment