Friday, 6 April 2018

Ana Shirin Daura Auren Wadanda Suka Sha Nono Daya A Sokoto

Cece-kuce ya biyo bayan wani aure na wadanda suka sha nono daya da ake shirin daurawa a jihar Sokoto.


Bincike ya nuna cewa uwar ango ta taba shayar da amarya nono lokacin da amaryar tana jaririya. Amma duk da jan hankalin da aka yi wa uban amaryar Aliyu Silame cewa yin hakan ya saba dokar musulunci amma ya yi kunnen uwar shegu, kamar yadda wata majiya daga 'yan uwan ma'auratan suka shaidawa RARIYA.

Za a daura auren na Abdulrazaq da amaryarsa Asma'u ne a gobe Asabar a unguwar Arkilla dake jihar Sokoto.
rariya.

No comments:

Post a Comment