Tuesday, 17 April 2018

Anyi bikin nuna kawa na farko a kasar Saudiyya

A makon jiyane aka yi bikin nuna kawa irinshi na farko a kasar Saudiyya, bikin wanda akayi mata ne zalla suka halarta, an hana maza 'yan gari dama maza masu daukar hotuna da masu kwalliya shiga gurin taron.

An nuna kayan kawa masu rufe jiki gaba daya da kuma wasu da sukayi kama da na kasashen yamma, rashin maza a gurin taron ya baiwa matan da suka halarci gurin cire nikabi da hijaban da suka saka, saidai kadanne daga cikin matan suka yarda suka cire hijabansu, kamar yanda jaridar Newyork Times ta ruwaito.


Wasu matan dai sun saka wanduna a gurin taron, kuma hadda wasu daga cikin 'ya'yan sarautar kasar ta Saudiyya sun halarci guein taron.

Kasar ta Saudiyya dai na amfani da shari'ar addinin musulunci amma 'yan kwanakinnan yarima Muhammad Bin Salman naso ya kawo canji akan yanayin zamantakewar kasar.

No comments:

Post a Comment