Tuesday, 3 April 2018

'Ba zamu dena magana akan kurakuren da akayi a mulkin Najeriya ba'>>Fadar shugaban kasa ta mayarwa da Obasanjo Martani

Fadar shugaban kasa, ta hannun daya daga cikin masu magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ta mayarwa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo martani akan maganar da yayi dangane da gwamnatin Buharin inda aka ruwaitoshi yana cewa gwamnatin ta gaza kuma ta cika korafi akan matsalolin Najeriya maimakon samo hanyar warwaresu.


Obasanjo ya kara da cewa kada 'yan Najeriya su sake mayar da wanda suka gaza mulki a lokacin da yake ganawa da wasu matasa da suka kaimai ziyara a gidanshi dake Abeokuta.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels, Femi Adesina ya bayyana cewa wannan maganar tuni ministan watsa labarai, Lai Muhammad ya bayar da amsa akanta a sanarwar da ya fitar kwanakin baya.

Amma ya kara jaddada cewa gwamnatin shugaba Buhari ba zata dena magana akan kurakuren da akayi a mulkin Najeriya ba a baya domin magance maimaita irin wadannan kurakuren a nan gaba.

Haka kuma ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta tabbatar da ganin anyi amfani da kudin da Najeriya take samu ba tare da almubazzaranci ba ta yanda yanzu gashi har ana da rarar kudi a asusun ajiya na waje da ba'a taba samun masu yawansu ba.

No comments:

Post a Comment