Tuesday, 17 April 2018

'Babu shakka Buharine zai sake cin zabe: Amma da ya gama ni zan karba'>>Rochas

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorochas ya bayyana cewa babu tantama shugaba Buharine zai sake lashe zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, kuma bayan shugaba Buharin ya gama mulkinshi to shine zai karba.


Ya bayyana hakane a lokacin da yake karbar bakuncin wasu masu ruwa da tsaki na harkar siyasar jihar, inda ya bayyana cewa bayan shugaba Buhari ya kammala mulkinshi, to shugabancin kasar zai koma kudu maso gabashin kasarnanne kuma shine zai zama shugaban kasa.
Vanguard.

No comments:

Post a Comment