Monday, 2 April 2018

Bani da burin tsayawa takarar shugaban kasa>>Saraki

Kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki ya musanta jita-jitar dake yawo cewa wai zai fito takarar shugaban kasa, a zaben shekarar 2019, da yake magana da jaridar Independent, me magana da yawun sarakin ya bayyana cewa wannan labari ba gaskiya bane.


Ya kara da cewa da Saraki na son fitowa takarar shugaban kasa, za'aji labarin a manyan jaridun kasarna, dan haka yayi kira ga mutane da suyi watsi da wancan labari.

Sanannen dan jaridar nan Dele Momodu ne ya bayyana cewa akwai alamu masu karfi dake nuna cewa sarakin na son tsayawa takarar shugaban kasa, labarin da ya watsu a tsakanin mutane.

No comments:

Post a Comment