Tuesday, 17 April 2018

Bankin Duniya ba zai bayar da bashi ga jihohin Najeriya ba idan babu jihar Kaduna a ciki

 
Gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa bashin da bankin Duniya zai baiwa jihohin Najeriya ba zai bayar ba idan babu jihar Kaduna a cikin, Gwamnan da mataimakinshi, Barnabas Bala Bantex ya wakilceshi a lokacin bude wani taron kungiyar Lauyoyi ta kasa a Barnawa dake Kaduna yace akwai siyasa a cikin kin amincewar da majalisar dattijai tayi na amsar bashin da jihar Kadunan zatayi daga bankin Duniya.

Gwamnan ya kara dacewa bankin Duniyan kanshi yayi mamakin yanda jihar Kadunace tafi cika dukkan sharuddan karbar bashin tsakanin jihohin dake neman bashin amma majalisa taki amince mata.

Ya kara da cewa kawai dan Sanatocin dake wakiltar jihar Kadunan na adawa da gwamnatin jihar ne yasa majalisar taki amincewa da cin bashin na jihar. The Cable.

No comments:

Post a Comment