Monday, 2 April 2018

Basaraken Yarbawa na shan suka bayan da ya canja sunan sarautarshi zuwa irin ta Hausawa

Basaraken masarautar Iwo dake jihar Osun, Oba Abudlrashid Adewale Akanbi ya hadu da fushin jama'ar Yarbawa bayan da aka zargeshi da canja sunan sarautarshi daga irin ta Yarbawa zuwa ta Hausawa.Kungiyoyin Yarbawa Irinsu Afenifere da sauran al-ummarsu sunyi ta sukarshi suna fadin wannan abin kunyane ya jawo musu.

Saidai a wata sanarwa da ya fitar ta hannun me magana da yawunshi ya bayyana cewa shi ba wai ya canja sunane daga Oba Zuwa Sarki ba, kawai dai ya fahimci da yawa daga Hausawa da suka fito daga Arewa basa iya fadin kalmar Oba daidai. Haka kuma idan yaje wani gari a Arewa yawanci mutane duk da sunan Sarki suke kiranshi, dan hakane ya ce Hausawa zasu iya rika kiranshi da sunan Sarki amma bawai ya canja sunan sarautar bane.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tayi magana da daya daga cikin fadawan dake aiki a fadar kuma shima ya kalubalanci maganar basaraken inda yace su 'ya'yan Oduduwane, amma yana fatan sauran mutanen su zasu saka basaraken nasu a addu'a dan ya caja ra'ayinshi akan wannan magana da yayi.

No comments:

Post a Comment