Thursday, 5 April 2018

Buhari Ya Amince Da Kashe Naira Bilyan 360 Don Sayo Makaman Yaki

A yau ne, bayan wani zama da manyan hafsoshin Sojan Nijeriya, Shugaba Muhammad Buhari ya amince da kashe sama da Naira Bilyan 360 don sayo makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da ayyukan ta'addanci.


Wadannan kudade dai, za a ciro su ne daga asusun rarar man fetur bisa amincewar gwamnonin Nijeriya, duk da yake tun da farko wasu daga cikin gwamnonin sun adawa da cire kudaden kamar yadda majalisar tarayya ta nuna rashin Jin dadinta kan rashin tuntubarta game da batun cire kudaden.
Rarriya.

No comments:

Post a Comment