Sunday, 1 April 2018

'Duk me kukan yunwa ya tashi ya nemi abinyi'>>Fadar shugaban kasa

Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu a wata hira da yayi da gidan talabijin na BEN ya bayyana cewa duk 'yan Najeriyar dake kukan yunwa su tashi tsaye su nemi aikin yi dan samun na kansu.


Malam Shehu ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari tana iya kokarinta wajan inganta rayuwar Al-ummar Najeriya ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da cigaba, yace sun samar da tsare-tsare na tallafawa gajiyayyu da kudin rage radadin talauci sannan sun baiwa harkar noma muhimmanci inda aka rika baiwa mutanen Najeriya kudin tallafin noma da sauran sana'o'i da babu ruwa ko kuma da ruwa dan kadan ta hanyar bankunan noma da babban bankin Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta ware kashi talatin na kudin shigarta wajan yin ayyukan raya kasa wanda a gwamnatocin da suka gabata ba haka abin yake ba, duka-duka abinda ake warewa ayyukan raya kasa befi kashi biyar cikin dari na abinda gwamnatin ke samu ba.

Ya kara da cewa kuma mutane zasu iya shaida hakan domin gashinan a fili ana ganin hanyoyin jirgin kass an ingantasu da kuma tituna da sauran kayan saukaka rayuwar al-umma, saboda haka duk wanda yake kukan yunwa ya tashi ya dena lalaci yaje ya nemi abinyi.

No comments:

Post a Comment