Tuesday, 3 April 2018

Fadakarwa akan kankan dakai daga Sheikh Isa Ali Pantami

 Sheikh Dr. Isa Ali Pantami yayi fadakarwa akan saukin kai kamar yanda lokaci zuwa lokaci yakan yi fadakarwa akan lamurran da suka shafi rayuwa da zaman takewar Al-umma. Malam ya fara da cewa, an umarcemu da kankan da kai da kuma gujewa girman kai domin samun nasara a rayuwar Duniya da Lahira. Kankan da kai yana kai mutum ga nasara, shi kuwa girman kai yana kai mutum ga tabewa.
Kankan da kai na daya daga cikin halayya ta gari, halayyace ta da take kan hanyar gaskiya. Nuna saukin kai ga mutane, da kuma kaucewa wulakantasu/nuna kafi su sabo da kabila, gurin zama, ko kuma wani matsayi da kake dashi, ko kuma ilimi.
Akan kankan da kai, annabi (S.A.W) yace, wanda yafi wani cikin masu Imani shine wanda yafi wani kyawun dabi'a, kankan da kai, wanda ya iya zama da mutane, babu Alheri a tattare da wanda be iya zama da mutane ba, suma kuma basu jin dadin zama tare dashi.Kankan da kai abun sone da yabawa, Shi kuwa girman kai abin zargine, jin cewa kafi kowa saboda wani abin Duniya daka samu abune me kaiwa ga halaka/tabewa, yana kuma kaiwa ga girman kai. Mutumin da ake wulakantawa/ana ganin cewa shi ba wani bane, zai iya zama mafi daukaka, amma me girman kai bazai ga hakan ba.

Jin cewa kaine akan gaskiya koda yaushe, sauran mutane kuma sune akan bata alamace ta girman kai, duk irin mukamin da gareka ra'ayinka zai iya zama daidai ko kuma akasin haka. Ka tuna da cewa babu ra'ayin wani da za'ace shine daidai a koda yaushe, a koda yaushe ka zama kana sauraren ra'yoyin/shawarwarin mutane.
Rashin ilimine da girman kai kesa mutum tunanin cewa ra'ayinshi/tunaninshi shine daidai a koda yaushe, kana kara samun ilimi, kana kara gano cewa abinda baka sani ba yafi wanda ka sani yawa, karka bata lokacinka/ko kuma kasancewa da mutumin da a koda yaushe ke tunanin cewa ra'ayinshi shine daidai.

No comments:

Post a Comment