Tuesday, 17 April 2018

Firaiministar Ingila tayi kiran hallata auren jinsi daya a Najeriya

Firaiministar kasar Ingila, Theresa May tayi kira ga Najeriya da sauran kasashe rainon Ingila dasu halatta auren jinsi daya, tayi wannan kirane a gurin taron kasashe renon Ingilar da akayi a yau, Talata acan kasar ta Ingila.


May ta bayyana cewa bata ga dalilin da zaisa a rika kyamar masu yin auren jinsi daya ba ko kuma a saka wata doka da zata rika hukuntasu ba kawai dan sunyi auren jinsi daya.

Ta kara da cewa yawancin dokokin dake hukunta masu auren jinsi daya a kasashe renon Ingila, Ingilar ce ta yisu lokacin mulkin mallaka, to yanzu kuma sun zama tsohon yayi dan haka ya kamata a faina amfani dasu.
The Cable.

1 comment:

  1. Lallai, toh shi Shugaba Buhari bai mata raddi ba ne?

    ReplyDelete