Thursday, 12 April 2018

Gaddafin Libya ne ya bai wa makiyaya makamai>> Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi tsohon shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi da bai wa makiyaya makamai a yankin Yammacin Afirka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya aike wa manema labarai a ranar Laraba.

Sanarwar ta kunshi bayanan da shugaban ya yi wa Archbishop na Canterbury Justin Welby ne, a kan dalilinsa na son sake tsayawa takara karo na biyu a ganawar da suka yi a birnin Landan.

Ya bayyana wa Mista Welby cewa rikicin manoma da makiyaya tsohon abu ne da aka dade ana fama da shi a kasar.

"Sai dai a yanzu ya yi muni ne saboda yadda 'yan bindiga daga yankin kudu da hamadar sahara ke kara kutsawa cikin yankin Yammacin Afirka," in ji shugaban.

Shugaba Buhari ya kara da cewa: "Mu'ammar Gaddafi na Libiya ne ya horar da wadannan 'yan bindiga. Da aka kashe shi kuma sai suka tsere da makamansu.

"Mun ga ire-irensu a yakin da muke yi da Boko Haram. Makiyaya da a baya mu ka san su da daukar sanda ko lauje don gyara hanyar wucewarsu kawai, amma wadannan na yanzu su na daukar mugayen makamai."
bbchausa.


No comments:

Post a Comment