Saturday, 14 April 2018

General BMB ya mayar da martani akan labarin dake cewa ya ruruta wutar gabar Ali Nuhu da Adam A. Zango

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya mayar da martani akan labarin da mujallar fim ta buga akanshi dake cewa, Ya ruruta wutar gabar Ali Nuhu da Adam A. Zango.Bello yace kamata yayi ace anji ta bakin dukkan bangarorin da abin ya shafa domin samun cikakken labarin, ya kara da cewa amma babu komai, hakan be dameshi ba dan yasan cewa dama mutum na kara samun cigaba yana kara samun makiya.

Kuma ya kara da cewa watakila labarin da aka buga a kanshi ya taimaka wajan sayar da kwafin mujallar da yawa.

No comments:

Post a Comment