Wednesday, 4 April 2018

Gwamnonin Jam'iyyar APC sun gana da shugaba Buhari

Gwamnonin jam'iyyar APC biyar, karkashin kungiyar gwamnonin sun gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Gwamnonin da sukayi ganawar sun hada da na Kano da na Imo da na Zamfara dana Flato dana Ogun.Bayan ganawar tasu gwamna Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara ya shaidawa manema labarai cewa gaba dayan gwamnonin APCn sun goyi bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan bin kundin tsarin mulkin jam'iyyar wajan samar da sabbin shuwagabanni.

A taron jam'iyyar da akayi a baya shugaba Buhari ya bukaci ayi zabe dan samar da sabbin shuwagabannin jam'iyyar, maimakon barin wadanda ke da mukamai yanzu suyi tazarce.

No comments:

Post a Comment