Friday, 13 April 2018

Jam'iyyar PDP ta baiwa Ummi Zeezee babban mukami

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Ibrahim Zeezee ta samu mukami daga jam'iyyar adawa ta PDP inda aka bata mukamin shugabar riko ta mata ta kungiyar dake yiwa PDPn kamfe gida-gida ta kasa baki daya.


Ummi da take bayyana wannan labari a dandalinta na sada zumunta da muhawara tace ta godewa Allah da wannan mukami da ta samu yau, kuma tana fatan Allah ya baiwa jam'iyyar ta PDP mulki a zaben shekarar 2019.

Ummi dai tayi suna wajan caccakar gwamnatin shugaba Buhari.

Wani shafi da ya wallafa wannan labari, me suna Authenticnewsdaily yace shugaban kungiyar yiwa PDPn kamfe gida-gida na kasane, Ibrahim Dahiru Danfulani ya tabbatar da wannan mukami na Ummi Zeezee a yau Juma'a.

Muna tayata murna da fatan Allah ya taya riko.

No comments:

Post a Comment