Monday, 2 April 2018

KA KULA DA ABOKAN KA>>Fadakarwa akan abota daga Sheikh Daurawa

ABOKIN KA SHINE WANDA BAZAI YI MAKA HASSADA BA, IDAN KA SAMU, KUMA BAZAI YI MAKA DARIYA BA IDAN KA RASA.
ABOKIN KA SHINE WANDA YAKE NUFIN KA DA ALKHAIRI. 
ABOKIN KA SHINE MAI YI MAKA FATAN ALKHAIRI,  A KO WANE LOKACI
ABOKIN KA SHINE MAI TAMBAYAR KA IDAN BAI GANKABA.
ABOKIN KA SHINE MAI KARBAR UZURIN KA.


ABOKIN KA SHINE ZAI BAKA SHI YA HAKURA. 
ABOKIN KA SHINE MAI SHIGA HATSARI DOMIN YA KUBUTAR DA KAI.
ABOKIN KA SHINE MAI KYAUTATA MAKA ZATO 
ABOKIN KA SHINE MAI GANIN KA DA MUTUNCI
ABOKIN KA SHINE MAI RAGE MAKA MAKIYA, YA KARA MAKA MASOYA.
ABOKIN KA SHINE WANDA YA DAMU DA KAI.
ABOKIN KA SHINE MAI BAKA KO SHI ZAI RASA.
ABOKIN KA SHINE MAI YI MAKA NASIHA, AKAN GASKIYA KO RANKA ZAI BACI. 
ABOKIN KA SHINE MAI NUNA FARIN CIKI DA CI GABANKA.
ABOKIN KA SHINE BAYA GULMAR KA, KO ZAGINKA A BAYAN IDONKA.
ABOKIN KA SHINE WANDA KA ZABA YA ZAMA ABOKIN KA, BA WANDA YA ZABE KA KA ZAMA ABOKIN SA BA.
ABOKIN KA SHINE WANDA KA TASIRANTU DA SHI, KO YA TASIRANTU DA KAI.
MANZON ALLAH SAW YACE KADA KAYI ABOKI SAI MAI IMANI.
ALLAH KA BAMU ABOKAI NA GARI, KA RABAMU DA MUGAYEN ABOKAI,  DA YAN TAYI DADI.

No comments:

Post a Comment