Thursday, 5 April 2018

Kalli irin kujerar da dalibai ke zama a wata makarantar kasar Amurka: Jama'ar gari sun tallafa bayan da wata malama a makarantar ta koka

Wannan irin yanda kujerun da daliban wata makaranta dake kasar Amurka ke zama kenan, malamar makarantar me suna Laurissa ce ta saka hoton kujerar a dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa irin kujerar da daliban da take koyawa karatu ke zama kenan, saboda karancin kujeru dole take zuwa da kujerar da ake nadewa daga gida, haka kuma ta kara da cewa ajujuwan sunwa daliban kadan.


Kwanaki biyar bayan da Laurissa ta bayyana irin yanayin da makarantar da take koyarwa take ciki sai jama'a suka fara bayar da kayan agaji zuwa makarantar, na kujeru da takardun rubutu, da yawa kuma suna ta tambayar ta wace hanya zasu iya bayar da tasu gudumuwar?.

Ya zuwa yammacin jiya dai darajar kayan tallafin da aka kai wannan makaranta sukai kimanin sama da naira miliyan goma sha biyar, kamar yanda CNN ta ruwaito kuma har yanzu ana cigaba da kawo tallafin.

Laurissadai tana daya daga cikin masu fafutukar inganta harkar ilimi a kasar ta Amurka inda kungiyarsu ke son a inganta albashin malamai da kuma samar da isassun kayan aiki a makarantu da yanayin karatu me kyau yanda dalibai zasu iya daukar darasi cikin yanayi me kyau.

Yayin da ta zo makaranta taga irin tallafin da mutanen gari suka bayar dalilin maganar da tayi, Malama Laurissa ta kasa hadiye murnarta inda har saida ta zubar da kwalla a gaban dalibanta dan murna.

Har yanzu dai mutane a kasar ta Amurka nata kara bayar da tallafi zuwa wannan makaranta.

No comments:

Post a Comment