Sunday, 15 April 2018

Kalli yanda wata uwargida ta shiryawa mijinta da Amaryarshi liyafa dan tayasu murnar aure

Wannan labarin wata uwargidace da rahotanni suka bayyana cewa ta shiryawa mijinta da amaryarshi liyafar ba zata dan tayasu murnar auren da sukayi, uwargidance a wannan hoton na sama take ciyar da amaryar abinci a baki.


Ba kasafai ake ganin mata na maraba da auren da mijinsu yayi ba ta irin wannan hanya, musamman saboda kishi, shiyasa wannan labari ya dauki hankulan mutane kuma da yawa sun yabawa uwargidan.

Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya da fahimtar juna.
hausaroom.

No comments:

Post a Comment