Friday, 6 April 2018

Kare kananan masana'antu da matasa yasa naki sawa yarjejeniyar kasuwanci hannu>>Shugaba Buhari

Da yake karbar wakilan kasashen Italiya da Andulus da kungiyar hadin kan kasashen turawa, a fadarshi, shugaba Buhari ya shaida dalilin da ya sa yaki amincewa da sa hannu a yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen yammacin Afrika dan ya kare kananan masana'antun kasarnan ne daga durkushewa da kuma kare matsa daga rasa ayyukan yi.Shugaba Buhari yace akwai kananan masana'antu da dama da suka samarwa matasan kasarnan ayyukan yi wanda idan aka sakawa waccan yarjejeniya hannu zasu samu kishiyoyin kamfunna daga kasashe da dama wanda ba lallai bane su iya karawa da su.

Hakan zai iya sawa kamfanonin su daina aiki kuma matasa su rasa ayyukan yi wanda gwamnati ba zata so hakan ba, shugaba Buhari yace burinsu shine su samarwa da matsa ayyukan yi ba abinda zai rabasa da ayyukan da suke yi ba su koma zaman kasashe wando shiyasa basu yarda suka sakawa wancan alkawarin kasuwanci hannuba.
Dailyturts.

No comments:

Post a Comment