Saturday, 14 April 2018

Karin Albishir Ga Magoya Bayan Shugaba Buhari

A 2015, Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC yayi nasarar lashe zaben Shugaban Kasa mai cike da tarihi, wannan nasara ta samu ne a dalilin irin gudunmawar da ‘yan Nigeria musamman matasa wajen tallata takarar ta sa sakamakon gamsuwa da amincewa da suka yi da shi.


Miliyoyin ‘yan Nigeria sun yi amfani da duk wata dama da suke da ita wajen tallata takarar Shugaba Buhari, sun yi amfani da kafafen sadarwa na zamani (Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp) domin aika sakonnin yakin neman zaben na sa.

Bayan samun nasara, Gwamnatin Shugaba Buhari ta fi maida hankali kan samar da tsaro wanda ta zo ta samu a tabarbare, bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, a wancan lokaci wadannan sune muhimman abubuwan da gwamnatin ta yi wa ‘yan Nigeria alkawura.

Ganin cewa da shafukan sadarwa na zamani aka yi amfani wajen cimma wannan nasara, hakan ta sa muke ganin ya fi dacewa gwamnatin ta sake amfani da wannan kafa domin sanarwa ‘yan Nigeria irin nasarorin da ta samu zuwa yanzu.

Haka kuma, a yayin da Shugaba Buhari ya sanar da zai sake tsayawa takara a shekarar 2019 a jam’iyyar APC, hakan ya sa ya zama dole a samar da wata dandali da zai ta tattaro dukkan ayyukan alheran da gwamnatin Shugaban Buharin ta gudanar don sanarwa jama’a dai-dai yadda za su fahimta tare da sanin tasirin ayyukan a rayuwar su ta yau da kullum.

Ofishina da wasu mutane da suke da alaka da ofishin na aiki kan wannan kafa da za ta tattara dukkan ayyukan da gwamnatin da gudanar kuma take kan gudanarwa. Mun yi amfani da tunani da hangen nesa wajen samar da wannan kafa kuma kafar za ta bawa kowa damar shigowa don tafiya da yin aiki kafada da kafada a tare. Kafar wani babban gida ne da zai wadaci duk wani magoyin bayan Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa.

Kwarai, gagarumin al’amari na nan tafe kwanan nan!

#PMBForNigeria 2019

Bashir Ahmad
Mai Taimakawa Shugaban Kasa
Kan Sababbin Kafafen Yada Labarai

No comments:

Post a Comment