Friday, 6 April 2018

Kasar China ta hana sayar da baibul

Kasar China ta haramta sayar da littafin bibul a shafukan yanar gizo, kasar ta bayar da wannan umarnine a wani shiri da take na dakile ayyukan addinan Musulunci da na Kiristanci inda tafi baiwa addinan Buddah dana gargajiya muhimmanci dan daukaka al-adun kasar.


Shafin the Australian ya ruwaito cewa neman littafin baibul na sayarwa a shafukan yanar gizo na sayar da litattafai beyi nasara ba bayan da aka kafa dokar, yayin da idan mutum ya nemi ya siya baibul din sai dai yaga wayam, babu komi.

Amma mutum zai iya samun baibul din a coci-coci da suran guraren Ibada.

No comments:

Post a Comment