Tuesday, 3 April 2018

Kasar Saudiyya ta saka dokar hana yiwa abokin zama bincike a waya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta saka dokar hana yiwa abokin zama, Mata ko miji bincike a waya dan kare sirrin 'yan kasa da kuma rage laifukan da ake yi ta kafar yanar gizo, ministan labarai na kasar ya bayyana cewa duk wanda aka kamashi da laifin yiwa abokin zamanshi bincike a waya za'a cishi tarar kwatankwancin Naira miliyan arba'in da bakwai.


Haka kuma zai yi zaman gidan kaso na shekara daya, kamar yanda Daily Mail ta ruwaito.

Wannan irin doka dai ta zowa wasu da mamaki domin ba kasafai ake jin irin taba a sauran kasashen Duniya.

No comments:

Post a Comment