Monday, 2 April 2018

'Kun cika raki>>Obasanjo ya caccaki gwamnatin Buhari

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin shugaba Buhari inda ya bayyanata a matsayin wadda ta cika raki da neman dorawa wasu laifi akan matsalolin da kasarnan ke ciki, Obasanjo ya bayyana hakane a lokacin da yake karbar bakuncin wasu matasa da suka ziyarceshi a gidanshi dake jihar Ogun.


Obasanjo ya bayyana cewa matasa ya kamata su tashi su nemi shugabanci da kansu bawai su rika jiran wani lokacin da bazai zo ba, ya kara da cewa Najeriya na bukatar mutane masu akida da sanin makamar aiki su mulketa ba irin wanda ake da su yanzu ba.

Ya kara da cewa masu mulkin yanzu sun cika raki inda suke ta cewa matsalar Najeriya ta yi yawa kuma suna zargin wasu bisa matsalolin na Najeriya, yace ai ansan da matsalar kuma abinda yasa ma aka zabesu kenan dan su samo hanyar warware matsalar Idan ba zasu iya bane sai su sauka.
Dailypost.

No comments:

Post a Comment