Sunday, 15 April 2018

'Kwankwaso na neman jam'iyyar da zai fito takarar shugaban kasa a ciki'

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shawara da makusanta da masoyanshi dan neman jam'iyyar da zai fito takara dan cimma burinshi na zama shugaban kasarnan.


Wani na kusa da kwankwason Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi ya bayyanawa jaridar Guardian hakan, inda yace kwankwason na neman shawarar na kusa dashi da kuma masoyanshi da masu ruwa da tsaki a tafiyarshi dan neman jam'iyyar da zai tsaya takarar neman kujerar shugaban cin kasarnan.

No comments:

Post a Comment