Monday, 9 April 2018

Kyan da ya gaji uban sa: Dan Ronaldo ya kwaikwayeshi

Dan gidan tauraron dan kwallo, Cristiano Ronaldo kenan a wadannan hotunan yake kokarin kwaikwayar irin abinda mahaifinshi yayi na cin kayatacciyar kwallo, Ronaldo dai yaci Juventus kwallo wadda ta dauki hankulan Duniya. To ga dukkan alamu danshi zai gajeshi.


A jiya, Lahadine gurin atisaye dan Ronaldon yayi wannan bajinta, kamar yanda Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment