Sunday, 8 April 2018

'Laifukan da PDP tayi a bayane ke bibiyarta'>>Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa irin laifukan da jam'iyyarsu ta PDP suka aikata a mulkin su ne yasa Allah ya kwace mulki daga hannunsu, dan haka ya shawarci 'yan jam'iyyar da su koma ga Allah su nemi gafara ko Al'amuransu zasu dawo daidai.


Bafarawa ya bayyana hakane a gurin taron PDPn na yankin Arewa maso yamma da akayi jiya a jihar Katsina, kamar yanda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito.

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo kuwa kira yayi ga 'yan Najeriya da su yi watsi da dabi'ar cin hanci da rashawa inda ya bayyana ta a matsayin abin kyama.

Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema kira yayi da a canja fasalin kasa inda yace hakan zai kawowa kasarnan cigaba cikin gaggawa.

No comments:

Post a Comment