Wednesday, 11 April 2018

Liverpool ta cire Man City ta kuma kafa tarihi: Salah ya kamo Eto'o a yawan kwallaye: Roma ta cire Barcelona

Liverpool ta kai zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko cikin shekara 10 bayan da ta doke Manchester City da 2-1 wato 5-1 jumulla bayan wasa biyu.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun Gabriel Jesus bayan sakan 116 bayan da Raheem Sterling ya ba shi kwallo.

Bernardo Silva ya daki turke kafin Sane ya ci kwallo amma aka hana saboda zargin satar gida duk da cewa James Milner ne ya taba kwallon.

Mohamed Salah ne ya rama wa Liverpool kafin Roberto Firmino ya ci ta biyu.

Liverpool za ta san kulob din da za ta kara da shi a ranar Juma'a lokacin da za a raba kungiyoyin a Nyon, na kasar Switzerland.

City ce ta mamaye kashin farko na wasan inda ta zubar da damarmaki, kafin Liverpool ta farfado a zagaye na biyu.


Alkalin wasa ya kora Pep Guardiola cikin 'yan kallo bayan da ya yi korafi kan hana kwallon da Sani ya ci a lokacin da aka ta fi hutun rabin lokaci.
bbchausa.

Wadannan kwallaye biyu da Liverpool taci jiya sun bata damar goge tarihin da Manchester United ta kafa, Shekaru goma sha biyar da suka gabata, inda yanzu Liverpool din take kan gaba a matsayin kungiyar kwallo daga Ingila dake da mafi yawan kwallaye a kakar wasan cin kofin zakarun turai da kwallaye talatin da uku.

Haka shima Muhammad Salah yaci kwallonshi ta talatin da tara a kakar wasa ta bana inda hakan ya bashi damar zuwa kankankan da tsohon tauraron kwallon kafa, Samuel Eto'o wanda shine dan Afrika da yafi yawan kwallaye a kakar wasan cin kofin zakarun turai da kwallaye takwas, yanzu Salah shima kwallayenshi takwas, idan ya samu ya sake cin wata kwallon a wasan kusa dana karshe da zasu buga, zai wuce Eto'o inda zai zama dan Afrika da yafi yawan cin kwallaye a kakar gasar cin kofin zakarun turai.

Barcelona tasha kashi a hannun A.S Roma inda Roman suka yi musu cin goge raini, 3-0 wanda gaba daya har wasan farko da suka buga ya tashi 4-4 kenan, Barcelona dai zata hada komatsenta ta koma gida daga gasar cin kofin zakarun turai na bana kenan.

No comments:

Post a Comment