Thursday, 12 April 2018

'Mafi yawan 'yan Najeriya sun gamsu da irin ayyukan da mukeyi: Shiyasa nake so naci gaba da mulki'>>Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce maganganun 'yan Najeriya ne suka sa ya bayyana aniyarsa ta sake neman takara karo na biyu a zaben shekara mai zuwa.


Da yake magana a lokacin da ya gana da shugaban mabiyar darikar Anglican Justin Welby, Buhari ya ce yana son ya mayar da hankali wurin bunkasa ayyukan noma da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa "Mafiya yawan 'yan Najeriya sun gamsu da irin ayyukan da mu ke yi, shi ya sa nake so na ci gaba da mulki".
bbchausa.

No comments:

Post a Comment