Saturday, 14 April 2018

Masu Unguwanni a Jihar Kaduna Za Su Fara Samun Alawus Duk Wata

Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince za ta fara biyan masu unguwanni 17,139 alawus duk wata don kara karfafa allurar rigakafi a jihar. 


Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne na fara biyan masu unguwannin da ake da su a masarautu 32 alawus na Naira 10,000 duk wata saboda irin gudummuwar da suke bayarwa wurin yakar cututtukan yara ta hanyar allurar rigakafin 

Wannan matakin da gwamnatin ta dauka ya biyo bayan irin ganin yadda Jihar Kaduna ta cire tuta wurin yaki da cutar shan- inna , kuma wannan nasarar tana da alaka da irin gudummuwar da wadannan masu unguwanni ke bayarwa. 

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta rika kashe kimanin Naira miliyan 171 duk wata don biyan kowane mai unguwa Naira 10,000 don kara karfafa musu gwiwa na irin gudummuwar da suke bayarwa da kuma dawo da martabar sarauta a jihar. 

Wannan sanarwar ta fito ne ta hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu , Farfesa Kabir Mato da Kwamishinan Lafiya, Dr Paul Manya A Dogo a zantawar da suka yi da manema labarai.

No comments:

Post a Comment