Tuesday, 17 April 2018

Matar da aka ajiye gawarta tsawon shekaru 4 saboda rikicin cewa musulmace ko kuwa A'A

An ajiye gawar wata mata a kasar Bangladesh bayan da ta kashe kanta amma ana rigima akan cewa musulmace kokuwa a'a, Hosne Ara Lazu ta musulunta a lokacin da ta auri, Humayun Farid Lazun, amma mahaifanta wanda mabiya addinin Hindune sun ki amincewa da auren inda har mahaifinta ya kai mijin kara gurin 'yan sanda inda yace be aura mishi diyarshi ba, sace ta yayi.


Ana cikin haka, Humayun dan shekaru 21 ya kashe kanshi a shekarar 2014, kasa da watanni biyu, itama matar tashi Hosne 'yar shekaru 18 ta sha guba ta mutu.

Bayan mutuwartane sai rikici ya barke tsakanin dangin mijinta da danginta, inda danginta sukace za'a mata jana'iza irinta mabiya addinin Hindu, domin kamin ta mutu ta bar addinin musulunci ta koma addinin Hindun.

Su kuwa iyayen mijin sukace a musulma ta mutu.

Wannan rikici nasu yaje kotu, aka yita shari'a kusan shekaru hudu kenan, sai satin daya gabata, sannan kotu ta yanke hukuncin cewa matar musulmace saboda haka a mata jana'iza irin ta addinin musulunci, kamar yanda NDTV ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment