Thursday, 5 April 2018

Muhammad Salah ya amince ya koma Real Madrid

Rahotanni daga kafar sadarwa ta kasar sifaniya me suna Don Balon na cewa tauraron dan kwallon kafa, Muhammad Salah ya amince ya koma bugawa kungiyar Real Madrid wasa a wani alkawari da suka kulla shi da me kungiyar Florentino Perez.


Tauraruwar Salah dai ta haskaka sosai a kakar wasa ta bana inda yaci kwallaye arba'in kuma manyan kungiyoyi irin su Real Madrid da Barcelona tuni suka fara kaimai hari dan daukeshi.

Wasu rahotannin na cewa Cristiano Ronaldo na daya daga cikin masu so Salah din yaje Madrid.

No comments:

Post a Comment