Monday, 2 April 2018

'Mutane zasu iya kare kansu'>>inji Gwamnatin tarayya

Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kariyar kai abune mekyau idan dai mutum be saba doka wajan yin hakan ba, ya bayyana hakane a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi.


Tsohon ministan tsaro T. Y Danjuma dai a satin daya gabata ya zargi jami'an tsaro da goyawa masu kashe 'yan Najeriya baya inda yace kowa ya tashi ya kare kanshi domin idan suka dogara da jami'an tsaron Najeriya to kuwa za'a kashesu, abinda jama'a da dama da gwamnati suka yi Allah wadai dashi.

A yanzu dai Garba Shehu ya bayyana cewa kariyar kai ba matsalabace matukar an yita bisa doka, kuma gwamnatin shugaba Buhari kofarta a bude take wajen sauraron shawarwarin mutane.

No comments:

Post a Comment