Thursday, 5 April 2018

Na ci Juventus kwallo mafi kayatarwa a tarihi>>Ronaldo: Amma tawa tafi kyau>>inji Zidane

media
Gwarzon dan kwallon duniya da ke take taka leda a Real Madrid, Christiano Ronaldo ya ce, kwallon da ya jefa a ragar Juventus a fafatawar da suka yi, ita ce kwallo mafi kyau da ya zura a tarihinsa na taka leda.


Kwallon ta gigita ‘yan kallo a Turin, in da hatta magoya bayan Juventus sai da suka mike tsaye don girmama Ronaldo saboda wannan cin da ya yi wa Gianluigi Buffon a wasan na dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai zagayen farko a Allianz.
Shi kan shi Buffon sai da ya cire safar hannunsa don jinjina wa Ronaldo mai shekaru 33.
Gianluigi Buffon and Cristiano Ronaldo
Ronaldo dai ya ci kwallaye da dama masu kayatarwa a wasannin da ya buga a kungiyoyi da kuma kasarsa ta Portugal, amma dan wasan ya yi amanna cewa, kwallon da ya zura a jiya ita ce mafi kayatarwa.
Dan wasan dai ya tashi sama sosai, in da ya bada tazarar kusan mita 3, sannan ya doki kwallon ta bayansa.
Real Madrid ce  ta yi nasara da ci 3-0 a fafatawar, in da Ronaldo din ya zura kwallaye guda biyu.

Daya daga cikin kwallo mafi kyua a tarihi

Golan Juventus Gianluigi Buffon: "Ronaldo dan wasa ne da ya kai makura... Za a iya kwatanta shi da Diego Maradona da kuma Pele."
Dan wasan baya na Juventus Andrea Barzagli: "Cristiano shi ya shirya kwallo ta biyu. Kai ka ce wasan kwaikwayo ne na kwamfuta... Kwallo ce da za a dade ana maganarta a tarihi. Abin takaici ne a kanmu lamarin ya faru".
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane: "Cristiano Ronaldo da ban ya ke a cikin saura. Kullum burinsa shi ne ya yi wata bajinta da babu wanda ya yi irinta a gasar Zakarun Turai. Kwallon da ya ci ta biyu abin al'ajabi ne, duk da cewa ya zubar da damarmaki biyu masu sauki. Haka kwallon kafa ta gada."
'Kwallon da na ci ta fi kyau'
Zinedine Zidane's stunning goal was at Glasgow's Hampden Park
Amma wacce kwallo ce ta fi kyau - bari mu bar maganar ga Zinadine Zidane wanda shi ma ya ci wata kwallo mai ban mamaki a wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da Real ta doke Bayer Leverkusen a 2002.
An tambaye shi ko wacce kwallo ce ta fi kyau, sai ya ka da baki ya ce...
Tawa mana! Hakika tawa ta fi.
rfihausa/bbchausa.

No comments:

Post a Comment