Tuesday, 17 April 2018

'Ni ba Bahaushiya bace: Ina jin dadin rayiwar aurena'>>Fatima Ganduje

Fatima Abdullahi Umar Ganduje diyace gurin gwamnan jihar Kano wadda kwanakin baya kadan akayi aurenta da mijinta, da daya namiji tilo a gurin gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi, shekarun Fatima 24 da haihuwa, ta kammala karatunta na jami'a da digiri me daraja ta daya daga jami'ar kasar Amurka dake jihar Adamawa, Fatima na da gidauniya data bude dan tallafawa mata da yara.


A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita, Fatima ta amsa wasu daga cikin tambayoyin da ya mata kamar haka:

Da alama kina jin dadin rayuwar aurenki?, Fatima ta amsa da cewa Eh, Tabbas hakane tun bayan da mukayi aure na kasance cikin farinciki a gidan mijina.

Shin zaki iya gaya mana yanda kuka hadu?, ta amsa da cewa dogon labarine amma a takaice, mun hadune sanadiyar wani dan uwanmu, kuma muna haduwa muka shaku da juna.

Zaki iya gayamana kalmar farko da ya fara gayamiki lokacin da kuka hadu?, ta amsa da cewa, ya cemin zan iya sanin ko ke wacece, sai na amsa da cewa Eh, me zai hana.

Tsawon wane lokaci kuka dauka kuna soyayya?, shekara daya da kusan rabi.

Shin zaki iya gayamana wane irin mutum ne mijinki?, ta amsa da cewa mijina mutumin kirkine yana kula dani kuma dukkan abinda nake nema a tattare da miji yana dashi.

Shin yaya kike kina kwalliya ki fito da kyau haka, tsawon wane lokaci kike dauka kina kwalliya?, sai ta amsa da cewa bana wani dadewa mintuna talatin kawai sun isheni, saboda nasan abinda zansa ya min kyau.

Shin yaya zaki bayyana 'yan uwan mijinki?, tace, suna son dan uwansu sosai kuma nima suna nunamin soyayya babu wani nuna banbanci.

Shin a matsayinki na bahaushiya yaya kikeji da kika auri bayerabe?, sai tace, Ni ba bahaushiya bace, ni bafulatanace.

Idan da ace bahaushe kika aura kina tunanin zaki samu babbanbancin soyayya?, sai tace ai soyayya ba ruwata da yare.

Kin iya yarbanci? , sai tace a'a nadai dan fara koyo(tayi wani yarbanci kadan) tace amma tana sa ran nan gaba zata iya sosai haddama abincin yarbawa duk tana so ta iya.

Ya zaki bayyana uwar mijinki?, tace mutuniyar kirkice tana mun abinda ya kamata, bama uwar mijin bace uwatace.
Thenet.ng

No comments:

Post a Comment