Friday, 13 April 2018

Real Madrid za ta kara da Bayern Munich: Liverpool zata kara da Roma


Real Madrid za ta kara da Bayern Munich a gasar zakarun Turai. yayin da Liverpool za ta kara da Roma.Za a yi wasannin a ranakun 24/25 na watan Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 1/2 ga watan Mayu.

Arsenal za ta kara da Atletico Madrid a wasan dab da na karshe na gasar Europa, yayin da Red Bull Salzburg za ta fafata da Marseille.

Za a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai a birnin Kiev, na Ukraine, ranar 26 ga watan Mayu.

Yayin da za a yi wasan karshe na Europa a birnin Lyon, na Faransa, a ranar Laraba, 16 ga watan Mayu.


Real Madrid ta fitar da Juventus a wasan dab da na kusa da na karshe, yayin da Roma ta fitar da Barcelona.

Ita kuwa Liverpool ta doke Manchester City, sai Bayern da ta yi waje da Sevilla.

A bara ma Real, wacce ke rike da kanbun, ta fitar da Bayern a kan hanyarta ta lashe gasar.
Bayern na kokarin lashe gasar a karon farko tun shekarar 2013.

Bayern ce za ta karbi bakuncin wasan farko, yayin da Roma za ta ziyarci Liverpool a wasan farko.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment