Saturday, 7 April 2018

Ronaldo ya sake cin irin kayatacciyar kwallon da ya ci Juventus

A yau, lokacin da yake atisaye tare da sauran 'yan kungiyarsu ta Madri, Cristiano Ronaldo ya sake cin irin kwallon da ya ci Juventus a wasan da suka buga na cin kofin zakaraun turai, Ronaldo ya tashi sama-sama ya daki kwallon da kafarshi ta wuce ta saman kanshi ta shiga raga.


The Sun sun ruwaito cewa irin kwallon da Ronaaldo yaci yau bata da banbanci da wadda yaci Juventus wadda saboda kyawunta hatta magoya bayan Juventus sai da suka tashi suna tafawa Ronaldon.

Da alama dai Ronaldon naso ya mayar da wannan sslon cin kwallonshi.

No comments:

Post a Comment