Tuesday, 24 April 2018

Sanata Dino Melaye ya diro daga motar 'yan sanda ya nufi daji da gudu

Sanata Dino Melaye kenan yayin da yayi tsalle daga motar 'yan sanda lokacin da suke tafiya dashi zasu kaishi jihar Kogi dan ya amsa tambayoyi akan zargin da ake mai na daukar nauyin wasu daya aika suyi kisa. 


Jami'an tsaro sun hana sanata Dino Melaye fita kasar waje yayin da yake yunkurin zuwa kasar Morocco gudanar da wani aiki, sannan kuma suka kewaye gidanshi dake Abuja, hakan yasa ya mika kanshi garesu.

'Yan sanda sun daukeshi suna tafiya dashi zuwa jihar Kogi dan yaje ya amsa tambayoyin zarginda ake mai sai yayi kogawa ya diro daga motar 'yan sandan ya nufi daji da gudu dalilin haka yaji raunuka wanda yanzu rahotanni ke nuna cewa an dawo dashi Abuja inda aka kaishi Asibiti dan duba lafiyarshi.

No comments:

Post a Comment