Thursday, 19 April 2018

Sanata Omo Agege yace bashi da hannu a sace sandar majalisa: Yanda Sanata Shehu Sani ya cire bel din kugunshi ya saka a madadin sandar majalisar: Tsageran sun so su sace wani sanata

Sanata Ovie Omo Agege dake wakiltar Delta ta tsakiya ne ake zargi da jagorantar sace sandar majalisar tarayya da akayi jiya, wasu rahotannin ma sun bayyana cewa wai shine ya dauko sandar da hannunshi ya mikawa tsageran da suka gudu da ita. Dalilin da ya sa akemai wannan zargi kuwa shine dakatarwar da majalisar ta mishi.Bayan sace sandar jami'an 'yan sanda sun tafi da sanatan inda ya amsa tambayoyi game da satar sandar, bayan fitowarshi ya bayyana cewa ya shaidawa 'yansandan cewa bashi da hannu game da satar sandar kuma maganar cewa wai shi ya dauko sandar ya baiwa tsageran duk karyane.
Sanata Omo ya kara da cewa maganar da me magana da yawun majalisar, Abdullahi Sabi yayi ta cewa yana da hannu a cikin satar da akawa sandar bata da tushe ballatana makama, kuma nan bada jimawaba zai bashi amsar da ta dace.

Bayan sace sandar a jiya, wasu rahotanni sun bayyana cewa Sanata Shehu Sani ya cire Bel din dake kugunshi ya saka a gurin da ake ajiye sandar, ya zama mamadin sandar dan majalisar taci gaba da zamanta, batun da shima ya dauki hankulan mutane har aka rika barkwanci a kanshi.

Daga baya dai an kawo wata sandar ta wucin gadi wadda ta baiwa majalisar damar ci gaba da zama.
punch, gurdian,the nation.

Indai wannan zargi da akewa sanata Omo Agege ya zama gaskiya to sai muce Allah ya baiwa, dan majalisar wakilai, Abdulmumini jibril hakuri.
A wani labarin kuma dake da dangantaka da wannan, tsageran da suka shiga majalisar tarayyar suka sace sandar majalisar sunso suyi garkuwa da wani sanata da ya fito daga jihar Legas me suna Solomon O. Adewale, ya bayyana a dandalinshi na shafin sada zumunta cewa ya sha da kyar a hannun tsageran yayin da suka turashi cikin wata mota da suka ajiye a gaban majalisar amma da Allah ya bashi sa'a ya ture kofar motar yayi tsalle ya fito waje.

Ya kara da cewa yana cikin koshin lafiya, yana dai amsar kulawa a hannun likitanshi.

Wani na kusa dashi yace sace shin da akayi niyyar yi baya rasa nasaba da maganar da yayi na cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da manyan jami'an tsaron kasarnan daga ayyukansu lura da irin rikice-rikicen da akeyi a kasarnan dake lakume rayuka.

No comments:

Post a Comment