Saturday, 14 April 2018

Shekara hudu da sace 'yan matan Chibok

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan sakandaren Chibok sama da 200 a garin Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Sama da 100 daga cikin 'yan makarantar da ake wa lakabi da 'yan Matan Chibok ne wala'allah suka tsere daga 'yan Boko Haram don radin kansu da wadanda dakarun kasar suka kubutar ta hanyar tattaunawar gwamnati da masu shiga tsakani.


Kungiyar Bring Back Our Girls na daga cikin wadanda suka fara gangamin matsin lamba ga gwamnnatin shugaba GoodLuck Jonathan da aka sace 'yan matan a lokacin mulkinsa, dan kubutar da su.

To amma an dauki lokaci har bayan shudewar gwamnatin Jonathan din babu wata ko daya daga cikin 'yan matan da aka kubutar.

A lokacin mulkin shugaba Buhari sojojin Najeriyar suka yi kicibis da daya daga cikin 'yan matan mai suna Amina Nkeke dauke da jaririyar da ta haifa bayan auren da ta yi da daya daga cikin mayakan da suka sace su.

A iya cewa sannu a hankali, tun daga bayyanar Amina sai hanya ta bude kuma ba a jima ba sai kungiyar Boko Haram, ta dinga fitar da bidiyon da ke dauke da 'yan matan na Chibok da kungiyar ta sace.

Bidiyon da ya fi daga wa gwamnati da iyayen yaran hankali, shi ne wanda ya nuna daya daga cikin matan sanye da shudin hijabi da farin nikabi, kewaye da wasu matan su kusan goma, tana magana.

Daya daga cikinsu, wacce ta yi jawabi a cikin bidiyon, ta ce ba za su koma wurin iyayensu ba. Ta yi kira ga iyayensu da su tuba, su yi mubaya'a ga kungiyar.

Sannu a hankali, adadin 'yan matan da aka kubutar da wadda aka tsinta suka tasamma sama da 100, sai dai har yanzu da aka cika shekara hudu cif da sace su wasu da dama ba a kubutar da su ba.

Boko Haram tana kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya ne tun shekarar 2009, kuma ta kai hare-hare kasashe masu makwabtaka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da 20,000 rikicin na Boko Haram ya hallaka, yayin da wasu dubbai suka yi hijira zuwa kasashe makofta. Wasu sama da miliyan daya ke jibge a sansanonin 'yan gudun hijira a ciki da wajen Najeriya.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment