Monday, 9 April 2018

Shugaba Buhari ya bayyana aniyarshi ta tsayawa takara a zaben 2019

Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019. Mai taimakawa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.


Bashir Ahmad ya ce zuwa an jima za a yi karin bayani kan lamarin.

Zuwa yanzu dai Shugaba Buharin da kuma gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar Ayo Fayose ne kawai suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasar.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment