Wednesday, 4 April 2018

Shugaba Buhari ya mika ta'aziyyarshi akan rasuwar sanata Mustafa Bukar

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hannun me magana da yawunshi, Malam Garba Shehu ya mika ta'aziyyarshi ta rasuwar margayi Sanata Mustafa Bukar me wakiltar Katsina ta Arewa wanda dan garin Daurane, Mahaifar shugaba Buhari, ga jama'ar jihar dama Najeriya baki daya.


Shugaba Buharin ya bayyana sanata Bukar a matsayin mutum me nuna kwazo wajan aiki da kuma dattaku, ya kara da cewa kwarewa da Sanata Bukar da yayi a aikinshi na Injiniyane yasa da ga ma'aikatar ruwa ta jihar Katsina ya samu aiki a ma'aikatar ruwa ta gwamnatin tarayya inda acan ma yayi aiki tukuru. Shugaba Buhari yace a koda yaushe yakan yi jimamin rashin mutane irin su Sanata Bukar masu kwazo da kishin kasa wajan aiki, haka kuma ya kara da cewa zasu yi amfani da irin salon aikin marigayin dan dora Najeriya a turbar cigaba.

A karshe yayi fatan Allah ya gafarta mishi ya sa gidan Aljannah ne makomarshi.

No comments:

Post a Comment