Monday, 16 April 2018

Shugaba Buhari zai gana da Trump da Theresa May

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai gana da shugaban kasar Amirka, Donald Trump ranar 30 ga watan Afrilun nan da muke ciki, wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban Amirkan ta White House tace ganawar ta shuwagabannin biyu zata kasancene akan dangantakar tattalin arziki da kuma batun tsaro.


Haka kuma wani rahoto daga jaridar Thisday na cewa shugaba Buharin zai gana da firaiministar kasar Ingila, Theresa May a yau, Litinin.

A makon da ya gabatane shugaba Buhari ya tafi kasar Ingilan dan halartar taron kasashe renon kasar Ingila da kuma tattaunawa da sauran manyan shuwagabanni.

No comments:

Post a Comment